Potato fried rice and meat fried rice with coloured eggs
Source : Ki Wanke Shinkafa Ki Dafa Karta Nina Saikiyi Per Boiled Ki Kara Mayarwa A Wuta Kisa Maggi Saiki Barta Ta Dahuki Dafa Kwai Ki Bare Kisa Colour Ga Kwara...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Umman Amir And Minaal
at : February 23, 2026
Step:
Ki wanke shinkafa ki dafa, karta nina saikiyi per boiled ki kara mayarwa a wuta kisa maggi saiki barta ta dahu
Ki dafa kwai ki bare, kisa colour ga kwara 2, 1 ki barshi haka nan
Ki yanka kayanki kamar haka, kiyi per boiled din carrot da peas, ki dafa dankali, ki dafa nama ki yanka kanana
Ki dora frying pan kisa mai da blue band kisa veggies dinki kisa maggi saiki juya sosai for 3 minutes, saiki raba biyu, rabi kisa dafaffen dankalin turawa, rabi kuma kisa nama wanda. Kika dafa da Maggie da curry, kika yanka kanana, na manta ban dauko na nama ba amma ga na dankali
Ki diba shinkafa kisa yellow food color ki juya sosai saiki dora frying pan a wuta kisa hadin nama kisa shinkafa ki juya sosai saiki bashi 3 minutes saiki sauke ki juye a kula.....haka zakiyi har ki gama na yellow color
Shima na green da hadin dankalin haka zakiyi har ki gama, sai kiyi designed din da kk so, kiyi garnishing da cucumber, colour egg dinki da tomato rose
Ingredients
Rice
Maggi
Food color (green and yellow)
Meat
Green pepper, peas, carrot, onions, scallions, red pepper