Source : Ki Tafasa Ruwa Idan Sun Tafasa Ki Wanke Shinkafa Ki Sa Ki Barta Ta Nuna Sosai Tayi Laushi Sai Ki Tuka Idan Yayi Ruwa Ki Daure Da Semo Sai Ki Kwashe A ...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Umman Amir And Minaal
at : January 9, 2026
Step:
Ki tafasa ruwa idan sun tafasa ki wanke shinkafa ki sa, ki barta ta nuna sosai tayi laushi sai ki tuka, idan yayi ruwa ki daure da semo sai ki kwashe a ledar tuwo
Ki gyara gyadar ki daka sosai, ki yi grating kayan miya, ki tafasa nama da maggi da curry da albasa
Ki soya mai da albasa idan ya soyu saikisa kayan miya idan sun fara soyuwa kisa nama da ruwan tafasar naman, saikisa maggi da curry da kayan kamshi ki juya
Idan ya tafasa kisa gyadar ki juya sosai saikisa alanyahu kisa jajjagaggen tarugu da albasa ki juya saiki rufe 4 5minutes saiki sauke shikenan.