Yadda ake hada awara(Tofu)

Source : A Gyara Wake A Cire Dattin A Wanke Shi A Rege Tsakuwar Da Kasar Da Ke Cikinsa Ya Fita Tass Sannan A Kai A Markado Idan Aka Markado Sai A Zuba Masa Manj...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : July 31, 2026

Step:

  1. A gyara wake a cire dattin.

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki1 hoto
  2. A wanke shi a rege tsakuwar da kasar da ke cikinsa ya fita tass, sannan a kai a markado.

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki2 hoto
  3. Idan aka markado sai a zuba masa manja a juya. Ana saka manja ne sbd yana yin kumfa

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki3 hoto
  4. A juya sosai sai a zuba ruwa a tace a kula kar a cika ruwa sosai yanda dai zai fita.

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki4 hoto Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki4 hoto
  5. A fitar da dusar

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki5 hoto
  6. Sai a juye a cikin tukunya babba sosai a dora akan wuta a dunga kula a barshi ya tafasa.

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki6 hoto
  7. Yana tafasowa za aga kumfa Tayi sama

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki7 hoto
  8. Sannan a sami ruwan tsami ko ruwan gasara a zuba akai

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki8 hoto
  9. Idan an zuba ruwan tsami za a ga tana hade jikinta

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki9 hoto
  10. Sai a barta ta karasa hadewa sannan a juye a abun tata a matse.

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki10 hoto
  11. Sannan a kulle bakin abin a dora mata abu me nauyi ta tsane sosai

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki11 hoto
  12. Idan ta tsane sai a yayyanka.

    Yadda ake hada awara(Tofu)matakin girki12 hoto

Ingredients

  1. Waken awara Rabin kwano (soya beans)
  2. 5 tbls Manja
  3. Ruwa
  4. Ruwan tsami/ ruwan gasara
  5. Abin tata

Related Recipes

Coconut basmati rice

Coconut basmati rice

Gireba

Gireba

Suya

Suya

Tayota/hikima

Tayota/hikima

Potato lollipop dankali me samfurin lollipop

Potato lollipop dankali me samfurin lollipop

Mummuki bread

Mummuki bread

Hadin daddawar miya na musamman

Hadin daddawar miya na musamman

Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambu

Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambu