Source : A Feraye Bayan Dankalin Ayi Masa Yankan Gida Huda A Zubashi A Cikin Ruwa Sannan A Wanka A Zuba A Tukunya A Zuba Ruwa A Dafashi Har Sai Ya Dahuwa Amma B...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : April 11, 2026
Step:
A feraye bayan dankalin ayi masa yankan gida huda a zubashi a cikin ruwa. Sannan a wanka a zuba a tukunya a zuba ruwa a dafashi har sai ya dahuwa amma ba luguf ba sai a tsane a kwalanda.
A dauko nikakken nama a wanke sannan dafashi da kayan kamshi, magi da albasa Idan ya dahuwa shima a ajiye guru daya Idan da ruwa a ciki a tsaneshi daga cikin ruwan.
A juye dankalin a roba me tsafta sai a marmasashi sannan a zuba naman a ciki, a kawo jajjagen a zuba, a saka kayan kamshi da kori kadan amma, sai a juya, Idan magi bejiba ba sai a kara a juya ya hade jikinsa.
A dunga mulmula hadin ana amaidashi kamar kwallo a ajiye a gefe, Idan yana kama Hannu sai a dunga dangwalar mai a hannun.
A Dora mai akan wuta a saka albasa, a sami kwano a fasa kwai a saka spices a yayyanka albasa kanana sai a kadashi sama sama..
Idan ya yi zafi sai a dauko dunkulen dankalin a saka shi a ruwan kwai sannan a barbadeshi da Garin burodi sannan a sake sakawa a ruwan kwai sai a saka a mai a soya. Idan ya koma ruwan Zuma sai a kwashe. A rage wutar sabida cikin ya soyu.
Idan aka kwashe man ya tsane sai a dauko tsinken tsire ko na sakace a soka a tsakiyar dankalin.