Lemon Zobo me inibi Danye.(zobarodo)

Source : Ga Dukkan Kayan Da Za Ayi Amfani Da Zu Nan A Sami Roba Me Tsafta A Zuba Zobo A Ciki Sannan A Zuba Ruwa A Girgijeshi Sai A Dunga Tsanewa Ana Zubawa A Tuk...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : April 12, 2026

Step:

  1. Ga dukkan kayan da za ayi amfani da zu nan.

    Lemon Zobo me inibi Danye.(zobarodo)matakin girki1 hoto
  2. A sami roba me tsafta a zuba zobo a ciki sannan a zuba ruwa a girgijeshi sai a dunga tsanewa ana zubawa a tukunya me tsafta, amfanin yin hakan sabida tsakuwa ko kasa su fita. Idan an gama sai a zuba ruwa daidai misali.

  3. A zuba kanumfari, masoro, kirfa, cardamom, danyar citta a gogata da manyan gida a zuba. Sannan a wanke na'a na'a a zuba akai sai a kara ruwa ya hau kan zobon sannan a Dora akan wuta a jefa yar kansa aciki sabida tsamin ya ragu a barshi yayi ta dahuwa Idan ya dahuwa sai a sauke.

    Lemon Zobo me inibi Danye.(zobarodo)matakin girki3 hoto
  4. A feraye bayan beetroot a yayyankashi kanana, a raba inibi 2 a cire kwallan sai a hada su guri daya a markada. Idan sun markadu sai a tace.

    Lemon Zobo me inibi Danye.(zobarodo)matakin girki4 hoto
  5. A wanke cucumber ma a yayyankashi kanana itama a markada ta, sai a tace a ajiye a gefe

  6. A samu babban Abu a tace zobon sai a kara ruwa a zuba ruwan beetroot da inibi hade da ruwan Cucumber a juya da majuyin katako sabida Kar yayi karni. A zuba sukari a juya sosai sannana a saka flavour Idan ana bukata a juya har sai yayi yanda ake so. A jefa kankara a ciki ko a saka a fridge yayi sanyi.

    Lemon Zobo me inibi Danye.(zobarodo)matakin girki6 hoto
  7. A zuzzuba a Kofi sai a saka yankakkiyar gurjin bature jikin kofin a kawo ganyen na'a na'a a sakala a jikin gurijin Baturen, a saka wata a cikin lemon. Sannan na jug din a saka inibi a gefe a kawo ganyen na'a na'a a sa a jiki.

    Lemon Zobo me inibi Danye.(zobarodo)matakin girki7 hoto
  8. Sannan ayi kwalliya da wasu daga cikin kayan hadin, yanada dadi kuma yana kara lfy

    Lemon Zobo me inibi Danye.(zobarodo)matakin girki8 hoto

Ingredients

  1. 1 Zobo Kofi
  2. Sukari daidai yanda zaiji
  3. Kanwa yar karama
  4. 8 Inibi guda
  5. 4 Na'a na'a wadda ba a tsinke ba guda
  6. 1 Icen kirfa karami
  7. Masoro 1/2 karamin cokali
  8. Kanumfari 1/2 karamin cokali
  9. 1 Danyar citta guda
  10. Cardamon 1/2 karamin cokali
  11. Filebo karamin cokaki 1 Dan bukata
  12. Beet root guda 1 karami
  13. 1 Gurjin bature madaidaici guda

Related Recipes

Cookies crumb ice-cream

Cookies crumb ice-cream

Wainar gero ta musamman

Wainar gero ta musamman

Butter icing

Butter icing

Cabbage roll

Cabbage roll

Jallop din shinkafa

Jallop din shinkafa

Cincin me laushi

Cincin me laushi

Spiced Crackers

Spiced Crackers

French toast + yam ball

French toast + yam ball