Source : Ga Kayayyakin Da Ake Bukataa Sami Tukunya Me Tsafta Sannan A Zuba Madarar A Ciki Sai A Zuba Ruwa A Damata Har Sai Ta Damu Ta Zama Babu Gudaji A Dora T...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : April 26, 2026
Step:
Ga kayayyakin da ake bukata
A sami tukunya me tsafta, sannan a zuba madarar a ciki, sai a zuba ruwa a damata har sai ta damu ta zama babu gudaji.
A Dora tukunyar madarar akan wuta a zuba kus-kus din akai a kawo sukari shima a zuba akai sai a fara juyawa sannan a barshi yayi ta dahuwa. A kula a zuba a tukunya me Dan girma sbd Idan ya tafaso zai zube.
Idan aka taba kus kus din akaji ya dahu za aga madarar ta danyi kauri.
A zuba fulawa a kwano a zuba ruwa a dama ta Kar tayi ruwa ruwa sannan Kar tayi kauri, sannan a zuba filebo a ciki a juya.
Idan ya damu babu gudaje sai a rage wutar a kawo damammiyar fulawar a zuba akan madarar a juya za a ga yayi kauri sai a kashe wutar ayi ta juyawa har sai ya hade ya zama Abu daya, za aji kamshi yanata tashi sai a sauke.
A wanke dabino a cire kwallayen sai a rarrabashi kanana. Sannan a zuba kunun a mazubi sai a kawo dabinon a watsa akai. A sha da zafinsa Idan ya sha iska bazai yi dadi sosai ba.