Source : A Gyara Wake A Cire Dattin A Wanke Shi A Rege Tsakuwar Da Kasar Da Ke Cikinsa Ya Fita Tass Sannan A Kai A Markado Idan Aka Markado Sai A Zuba Masa Manj...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : July 31, 2026
Step:
A gyara wake a cire dattin.
A wanke shi a rege tsakuwar da kasar da ke cikinsa ya fita tass, sannan a kai a markado.
Idan aka markado sai a zuba masa manja a juya. Ana saka manja ne sbd yana yin kumfa
A juya sosai sai a zuba ruwa a tace a kula kar a cika ruwa sosai yanda dai zai fita.
A fitar da dusar
Sai a juye a cikin tukunya babba sosai a dora akan wuta a dunga kula a barshi ya tafasa.
Yana tafasowa za aga kumfa Tayi sama
Sannan a sami ruwan tsami ko ruwan gasara a zuba akai
Idan an zuba ruwan tsami za a ga tana hade jikinta
Sai a barta ta karasa hadewa sannan a juye a abun tata a matse.
Sannan a kulle bakin abin a dora mata abu me nauyi ta tsane sosai