Source : A Wanke Tukunya Sai A Zuba Ruwa A Rufe Sannan A Dora A Kan Wuta A Wanke Kayan Lambun Da Ruwan Gishiri A Yanka Dogon Wake Karas A Kankare Bayan Sannan ...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : April 30, 2026
Step:
A wanke tukunya sai a zuba ruwa a rufe sannan a Dora a kan wuta.
A wanke kayan lambun da ruwan gishiri, a yanka dogon wake, karas a kankare bayan sannan a yayyanka shi shima a hade guri daya da sauran a ajiye a gefe.
A zuba gishiri cokali 1 a shinkafa sannan a zuba ruwa a wanketa tass. (Amfanin wankewa da gishiri yana fitar da starch sannan yana sawa tayi wara wara Idan an dafa)
Idan ruwan ya tafasa sai a zuba shinkafar a ciki a juya a rufe
A kula Idan shinkafar tayi tafasa 2 sai a kawo kayan lambun a zuba akai su karasa dahuwa tare. Idan ta dahu sai a zuba ruwa a wanke a tace sannan a maidata kan wuta ta turaru na minti 5 sai a sauke
A zuba a mazubi aci da kowacce miyar da ake bukata.