Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambu

Source : Da Farko Za Mu Fara Da Gyara Kayan Lambun Mu Mu Wanke Mu Yayyanka Mu Ajiye A Gefe Sannan A Dora Mai Akan Wuta A Saka Albasa Idan Yayi Zafi Sai A Zuba Ta...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : November 27, 2025

Step:

  1. Da farko za mu fara da gyara kayan lambun mu mu wanke mu yayyanka mu ajiye a gefe.

    Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambumatakin girki1 hoto
  2. Sannan a Dora mai akan wuta a saka albasa Idan yayi zafi sai a zuba taliyar (makaroni) a soya har ta zama ruwan zuma

    Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambumatakin girki2 hoto
  3. Sannan a kwashe a kwalandar karfe man ya tsane.

    Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambumatakin girki3 hoto
  4. A Dora tukunya akan wuta a zuba mai Dan kadan sannan a kawo albasa a saka Idan yayi zafi sai a dauko nama wanda dama an tafasa shi da kayan kamshi. A zuba akai a juya kamar mintuna 5 sai a kawo jajjagen attaruhu da albasa a zuba akai a juya a soya sama sama. Sannan a tsaida ruwa

    Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambumatakin girki4 hoto
  5. A zuba curry, spices, tafarnuwa da maggie

    Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambumatakin girki5 hoto
  6. A rufe mintuna 10 sai a zuba kayan lambu a rufe.

    Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambumatakin girki6 hoto
  7. A barshi ya tafasa kayan lambu su Dan fara laushi, sai a dandana Idan komai yaji sai a kawo makaronin a zuba akai a rufe a barshi ya dahu

    Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambumatakin girki7 hoto
  8. A juya a rufe

    Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambumatakin girki8 hoto
  9. A zuba a ci da zafinata

    Jallop din soyayyiyar makaroni me kayan lambumatakin girki9 hoto

Ingredients

  1. Leda 3 ta taliya(makaroni)
  2. Jajjagen attaruhu da albasa daidai misali
  3. Maggie domin dandano
  4. 2 Mai ludayi
  5. Tafarnuwa domin bukata
  6. Kayan kamshi (spices)
  7. Curry
  8. 1 Koren wake Kofi
  9. 1 Mulmulallen wake Kofi
  10. 1 Albasa madaidaiciya guda
  11. 5 Karas manya guda
  12. Mai domin suya

Related Recipes

Gireba

Gireba

Coconut basmati rice

Coconut basmati rice

Spiced Crackers

Spiced Crackers

Butter icing

Butter icing

Tart din dambun nama

Tart din dambun nama

Almond fried Egg

Almond fried Egg

Onion and mince meat sauce

Onion and mince meat sauce

French toast + yam ball

French toast + yam ball