Source : Da Farko Zaki Dora Ruwanki Awutasai Ki Wanke Shinkafarki Ki Tsaneta Sosai Kidan Baza Tasha Iskaidan Ruwan Ya Tafasa Sai Ki Kawo Shinkafarki Ki Zuba Ki D...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Umman Amir And Minaal
at : May 13, 2026
Step:
Da farko zaki dora ruwanki awuta Sai ki wanke shinkafarki ki tsaneta sosai kidan baza tasha iska
Idan ruwan ya tafasa sai ki kawo shinkafarki ki zuba ki dan motsa da muciya saiki rufe kibashi minti arba'in Idan yayi sai ki tukeshi ki kawo leda kina kullawa
Ki wanke albasa ki yayyanka kanana tare da tumatiri, sai ki daura mai a wuta ki zuba su a ciki. Ki yi jajjagen tarugu da tattasai da citta da tafarnuwa ki zuba
Saiki tsaida ruwa kisa nama ko kifin, kisa maggi da kayan kamshi, ki rufe kibarshi ta dahu
Saiki wanke alanyahu ki yanka ki kara wankewa ki daka, ko ki nikashi a bilenda, sama sama, saikisa alanyahun
Ki rufe ki rage wuta, idan yayi minti biyar saiki sa jajjagaggen tarugu da albasa, ki bashi minti biyu saiki sauke shikenan