Dambun shinkafa me naman kaza

Source : Bayan An Barzo Mini Shinkafa Sai Na Diba Daidai Yanda Zaici Steamer Din Na Wanke Da Ruwa Na Tsane Ruwan Sannan Na Zuba Soyayyen Mai Kamar Cokali 3 Na ...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : May 6, 2026

Step:

  1. Bayan an barzo mini shinkafa sai na diba daidai yanda zaici steamer din, na wanke da ruwa na tsane ruwan. Sannan na zuba soyayyen mai kamar cokali 3 na sa Maggie shima ba da yawa ba da Dan gishiri kadan na jujjuya na jefa icen kirfa sannan na juye a cikin steamer din dama na Dora akan wuta ruwan ya yi zafi sai na sa buhu a saman na rufe da murfin sannan na Dora Abu me nauyu.

    Dambun shinkafa me naman kazamatakin girki1 hoto
  2. Bayan ya turaru sai na juyeshi a babbar tukunya na marmasashi ya zama babu gudaje ya yi warawara.

    Dambun shinkafa me naman kazamatakin girki2 hoto
  3. Sannan na zuba magi, curry, spices hade da dakakkiyar gyada, da tafarnuwa Idan ana bukata na juya

    Dambun shinkafa me naman kazamatakin girki3 hoto
  4. Sai na zuba yankakkiyar albasa, jajjagen attaruhu da albasa hade da zogale shima na juya

    Dambun shinkafa me naman kazamatakin girki4 hoto
  5. Daga nan na kawo tsokar kaza wadda na tafasata da kayan kamshi da Maggi nayi mata yankan kanana banda kashi na zuba na juya.

    Dambun shinkafa me naman kazamatakin girki5 hoto
  6. Sannan na kawo ruwan tafashen kazar da na'a na'a na zuba akai na juya suka hade na dandana naji komai yaji sai na mayar cikin steamer din ya karasa turaruwa. Idan yayi zakiji kamshi na musamman yana tashi sai ki juye a roba ko tukunya.

    Dambun shinkafa me naman kazamatakin girki6 hoto
  7. Sai ki zuba soyayyen mai Wanda yaji albasa akai ki cire icen kirfa din sannan ki juya sai a zuba a ci da zafinsa yafi dadi. Kyanta akwai lemon tsamiya me hadin danyar citta a kusa....

    Dambun shinkafa me naman kazamatakin girki7 hoto

Ingredients

  1. 1 Barzajjiyar shinkafa kwano
  2. Zogale cikin madaidaicin baho
  3. 1 Attaruhu da albasa jajjage robar ice cream
  4. Maggie yanda zaiji
  5. Gishiri kadan
  6. 4 Gyada gwangwani
  7. 4 Curry cokali
  8. 2 Spices cokali
  9. 2 Na'a na'a cokali
  10. 2 Icen kirfa madaidaita guda
  11. Kazar gidan gona guda 2 manya
  12. Mai
  13. Tafarnuwa domin bukata

Related Recipes

DIY Condensed milk

DIY Condensed milk

Steam moimoi Alala

Steam moimoi Alala

Almond fried Egg

Almond fried Egg

Noodles

Noodles

Gireba

Gireba

Spiced Crackers

Spiced Crackers

Shawarma

Shawarma

Fresh ginger and lemon juice

Fresh ginger and lemon juice