Farfesun naman karamar dabba

Source : A Sami Roba A Juye Naman Sai A Gyara Shi A Rage Masa Kitse Idan Yankan Manya Ne A Yayyanka Ya Dawo Madaidaita Sai A Zuba Ruwa A Yanka Lemon Tsami A Wan...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : May 27, 2026

Step:

  1. A sami roba a juye naman sai a gyara shi a rage masa kitse Idan yankan manya ne a yayyanka ya dawo madaidaita. Sai a zuba ruwa a yanka lemon tsami a wanke sosai da Sosai.

  2. A juye a tukunya a Dora a wuta, sannan a zuba yankakkiyar albasa, curry, kayan dandano, kayan kamshi, citta sannan a daka tafarnuwa a zuba Idan ana bukata a zuba wadataccen ruwa a rufe yayi ta dahuwa.

  3. Idan ya dahu ruwan ya zama Rabi sai a zuba mai, attaruhu da albasa a Dan kara kayan kamshi Idan magi bejiba ba a kara sai sake rufewa.

  4. Mintuna 10 sai a kawo yankakken Koren tattasai da albasa a zuba akai a rufe sai a kashe wutar. Minti 5 da saukewa sai a kwashe. An fison sa da romon romo.

    Farfesun naman karamar dabbamatakin girki4 hoto

Ingredients

  1. Naman karamar dabba
  2. Jajjagen attaruhu da albasa Wanda aka tafasa
  3. Tafarnuwa domin bukata
  4. Mai kadan
  5. Lemon tsami
  6. Kayan dandano
  7. Kayan kamshi
  8. Curry
  9. Dakakkiyar citta wadda taji kayan hadin gargajiya
  10. Koren tattasai
  11. Yankakkiyar albasa

Related Recipes

Shawarma

Shawarma

Wainar fulawa

Wainar fulawa

Cincin me laushi

Cincin me laushi

Special cookies

Special cookies

Dambun kaza me dadi

Dambun kaza me dadi

Gasashshen meat pie

Gasashshen meat pie

Steam moimoi Alala

Steam moimoi Alala

Egg roll

Egg roll