Bun's din alkama da fulawa me chakuleti

Source : A Hada Garin Fulawa Da Alkama Guri Daya A Jujjuya Har Su Hade A Zuba Bota Yist Sukari Madara A Jujjuya Sannan A Zuba Ruwan Dumi A Kwaba Kada Kwabin...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : April 1, 2026

Step:

  1. A hada garin fulawa da alkama guri daya a jujjuya har su hade.

    Bun's din alkama da fulawa me chakuletimatakin girki1 hoto
  2. A zuba bota, yist, sukari, madara, a jujjuya sannan a zuba ruwan dumi a kwaba, kada kwabin yayi ruwa kuma kada yayi tauri. Kwabin yafi na meat pie ruwa, sannan a rufe a ajiye a GU me dumi.

    Bun's din alkama da fulawa me chakuletimatakin girki2 hoto
  3. Tsawon mintuna 30 zuwa 45 a dauko za aga ya tashi ya ninka na farkon a yawa

    Bun's din alkama da fulawa me chakuletimatakin girki3 hoto
  4. Sannan a zuba fulebo na vanilla a juya

    Bun's din alkama da fulawa me chakuletimatakin girki4 hoto
  5. A zuba mai a kaskon suya a yanka albasa Idan ya fara zafi sai a kwashe albasar, a debo kwabin a buda tsakiyar sai a saka chakuletin a ciki a rufe ana mulmulawa har ya hade, a dunga dangwalar ruwa Idan yana makalewa a hannu sannan a sa a mai a soya.

    Bun's din alkama da fulawa me chakuletimatakin girki5 hoto Bun's din alkama da fulawa me chakuletimatakin girki5 hoto
  6. A kula Kar a cika masa wuta, wuta kadan za a saka sabida cikin ya soyu, Idan an saka sai a dunga juyawa har ya zama ruwan Zuma me turuwa sannan a kwashe.

    Bun's din alkama da fulawa me chakuletimatakin girki6 hoto
  7. A sami tsinken yin tsire a sossoka buns din a ciki Sabida ya bada abin shaawa. A ci da lemo ko acishi hakanan.

    Bun's din alkama da fulawa me chakuletimatakin girki7 hoto

Ingredients

  1. 1 Fulawa Kofi
  2. 1 Garin alkama Kar ya karasa Kofi
  3. Madarar gari babban cokali 2
  4. Yist babban cokali 1
  5. Sukari babban cokali 3
  6. cokali Vanilla filebo Rabin karamin
  7. Alawar chakuleti
  8. Mai
  9. Bota babban cokali 1
  10. Ruwan dumi
  11. Tsinken yin tsire

Related Recipes

Bread crumb akara

Bread crumb akara

Juice din lemon Zaki da karas

Juice din lemon Zaki da karas

Tsiren naman karamar dabba

Tsiren naman karamar dabba

Peanut burger 2

Peanut burger 2

Macaroni salad

Macaroni salad

Steam RVC

Steam RVC

Spiced Chips with onion and egg sauce

Spiced Chips with onion and egg sauce

Noodles

Noodles