Source : A Fara Da Soya Taliya Da Macaroni A Tsane A Ajiye A Gefesannan A Daura Mai Akan Wuta A Yanka Albasa Idan Yayi Zafi Sai A Zuba Jajjage A Motsa Sannan A Z...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : December 3, 2025
Step:
A fara da soya taliya da macaroni a tsane a ajiye a gefe
Sannan a daura mai akan wuta a yanka albasa Idan yayi zafi sai a zuba jajjage a motsa.
Sannan a zuba soyayyen nama akai
A juya a tsaida ruwa da ruwan zafi a saka kayan kamshi
Sannan a saka curry
A saka maggie da tafarnuwa sai a rufe a barshi ya tafasa
Idan ya tafasa sai a dandana aji Idan komai yaji sai a kawo taliya da makaronin a zuba akai a juya a rufe
A barta ta dahuwa kada a cika wuta, Idan ta kusa dahuwa sai a kawo dambun nama a zuba akai a Dan motsa kadan
A yayyanka alayyahu da albasa yankan manya a wanke sai a zuba a juya su hade sai a kashe wutar, turirin abincin zai sa alayyahun ya dahu.
Sai a sauke a zuba a ci da zafinta. Ita makaroni ko takiya cinsu da zafi yafi dadi