Source : To Uwargida Da Farko Ki Gyara Wakenki Ki Wanke Ki Zuba A Tukunya Ki Dora A Wuta Idan Kin Duba Waken Ya Kusa Nuna Sai Ki Wanke Shinkafarki Tas Sannan K...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Umman Amir And Minaal
at : March 24, 2026
Step:
To uwargida, da farko ki gyara wakenki ki wanke ki zuba a tukunya ki dora a wuta. Idan kin duba waken ya kusa nuna sai ki wanke shinkafarki tas, sannan ki zuba a kan waken sai ki sa gishiri ki rufe.
Sai ki dauko salat dinki ki wanke da gishiri, sannan ki yanka, ki wanke tumatir da albasa suma ki yanka ki ajiye a gefe.
Sai ki duba Idan shinkafarki tadahu sai ki sauke. Ki soya man gyada da albasa.
Sai ki zuba a kula ko a filet ki sa manki, da su salat, da maggi, da yajinki sannan a ci.