Source : Zaki Jika Wakenki Kamar 3 Hours Saiki Kai A Markada Idan Aka Markada Sai Ki Tace Ta Da Kyallen Taci Saikisa A Wuta Har Ya Tafasa Saiki Sa Ruwa Tsaminki...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Umman Amir And Minaal
at : December 8, 2025
Step:
Zaki jika wakenki kamar 3 hours saiki kai a markada Idan aka markada sai ki tace ta da kyallen taci saikisa a wuta Har ya tafasa, saiki sa ruwa tsaminki zakiga ruwa yana kwantawa awarar Tana tasowa sai ki kwashe a kyallen da kika tace ki daure ki rataya a wani gurin domin ruwan ya tsane
Bayan ruwa ya tsane sai ki yayyanka yanda kikeso saiki jika Maggi da dan gishiri a ruwa, ki zuba awarar a CIKI, saiki dora mai a wuta Idan ya yi zafi saiki cire awarar a ruwa kisa a mai Idan ya soyu saiki kwashe, haka zakiyi tayi Har ki gama suya
Zaki yanka Tumatir kanana ki jajjaga tarugu da tattasai da albasa Idan ya yi sai ki soya mai kisa Kayan miyarki da Maggi da salt and curry kiyita juyawa Har ya soyu saikisa a awarar ki juya ki yanka cabbage ki zuba ki kara juyawa shikenan, acidadi lafiya