Fish rolls

Source : Zaa Sami Flour A Zuba A Roba Sai A Kawo Sugar Salt Egg Baking Powder Da Butter A Cakuda Sosai Har Sai Komai Ya Hade Sai A Kawo Ruwa Mai Sanyi A Zuba A...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : August 11, 2026

Step:

  1. Zaa sami flour a zuba a roba sai a kawo sugar, Salt,egg baking powder, da butter a cakuda sosai har sai komai ya hade sai a kawo ruwa mai sanyi a zuba a juya sosai har sai ya hadu sannan a fadada da rolling pin. A rufe da kitchen towel a aje a gefe.

  2. A sami kifi mai kyau a gyarashi sannan a wanke da lemon tsami ko vinegar sannan a tafasa shi. Idan ya huce sai a cire kayoyin sannan a marmasa a aje a gefe.

  3. Zaa dauko attaruhu a wanke a jajjaga, a wanke albasa da tattasai a yankasu yadda akeso sai a zuba mai a kasco kadan idan yayi zafi sai a zuba albasar a juya daga nan sai a zuba attaruhu da tattasai a juya, a zuba magi thyme, curry a juya sai a kawo marmashen kifin a zuba a yi ta juyawa har sai yayi sai a sauke.

  4. Idan ya huce sai a dauko kwababban fulawar da aka fadada a zuba hadin kifin daga gefe sai a nannada kamar tabarma anayi ana shafa ruwa jikin fulawar har a gama sai a saka wuka a rarraba, a jera a farantin gashi sai a shafa ruwan kwai a saman sannan a gasa.


Ingredients

  1. Flour kofi
  2. Kifi
  3. Attaruhu
  4. Albasa
  5. Maggi
  6. Curry
  7. Thyme
  8. Baking powder
  9. Salt
  10. Butter

Related Recipes

Lemon karas

Lemon karas

Dambun shinkafa

Dambun shinkafa

Simple beef soup

Simple beef soup

Pommo stew

Pommo stew

Spicy potato chips

Spicy potato chips

GarauGarau

GarauGarau

Potato porridge

Potato porridge

Chicken pepper soup

Chicken pepper soup