Hikima(tayota)

Source : Da Farko Zaki Samu Roba Meh Zurfi Ki Zuba Fulawa Madara Gishiri Da Baking Powder Seh Ki Juya Su Hade Seh Ki Rika Zuba Ruwan Kadan Kadan Kina Juyawa Da W...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : April 1, 2026

Step:

  1. Da farko zaki samu roba meh zurfi ki zuba fulawa,madara,gishiri,da baking powder seh ki juya su hade.seh ki rika zuba ruwan kadan kadan kina juyawa da whisk har yayi kaurin da kike so amma karyayi tsululu kuma kar yayi kauri dayawa.

    Hikima(tayota)matakin girki1 hoto Hikima(tayota)matakin girki1 hoto Hikima(tayota)matakin girki1 hoto
  2. Bayan kin juya ya hade sosai ba gudaji seh ki dora mai kan wuta ki saka karfen hikiman a ciki suyi zafi tare.idan man yayi zafi seh ki cire karfen a ciki ki tsoma cikin kullin seh ki saka shi cikin mai.

    Hikima(tayota)matakin girki2 hoto Hikima(tayota)matakin girki2 hoto Hikima(tayota)matakin girki2 hoto
  3. Seh ki dan jijigashi kadan a ciki a hankali zaki ga yana fita daga karfen kina jijigawa kadan kadan har ya fita gaba daya.Amma wajen tsomawa cikin kullin kar ki tsoma karfen gaba daya kullin ya rufe shi idan ba haka ba ba zeh fita yadda akeso ba iya cikin karfen amma kar ya tsomu har sama.

    Hikima(tayota)matakin girki3 hoto Hikima(tayota)matakin girki3 hoto
  4. Kina yi kina juya wanda suka fara ja,idan sun soyu sun yi ja seh ki kwashe ki sa wasu har ki gama.

    Hikima(tayota)matakin girki4 hoto

Ingredients

  1. kofi 4 na fulawa
  2. Madara babban chokali 4
  3. Gishiri karamin chokali 1
  4. Baking powder karamin chokali 1
  5. Ruwa dai dai bukata
  6. Mai na suya
  7. Karfen hikima
  8. Sikari 1/4 kofi(kina iya karawa yadda kike son zakin)

Related Recipes

Hanjin ligidi

Hanjin ligidi

Crunchy peanut cookies

Crunchy peanut cookies

Pizza sauce

Pizza sauce

Kunun zaki

Kunun zaki

Faten wake da plantain

Faten wake da plantain

Pateera

Pateera

Peanut burger

Peanut burger

Dan wake

Dan wake