Miyar gyada

Source : Ki Samu Frying Pan Sai Ki Soya Gyadarki Sama Sama Da Wuta Kadan Yanda Bawonta Zai Fita Da Sauki Sai Ki Juye A Tray Ta Sha Iska Sai Ki Murje Ki Bakace S...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : January 22, 2026

Step:

  1. Ki samu frying pan sai ki soya gyadarki sama sama da wuta kadan yanda bawonta zai fita da sauki, sai ki juye a tray ta sha iska sai ki murje ki bakace sai ki daka ki aje a gefe.

  2. Ki zuba manja a tukunya sai ki zuba garlic da ginger sai ki zuba albasa idan ya dan soyu kadan sai ki zuba gyada ki dan soya ta kadan a low heat sai ki zuba kayan miya ya dan soyu.

  3. Idan kayan miyan ya soyu sai ki zuba nama da ganda da ruwan tafashe ki sa daddawa da crayfish da seasoning da maggi sai ki dan kara ruwa if needed sai ki barshi ya dan kara dahuwa

  4. Idan miyarki ta soyu mai ya dan fito a saman sai ki zuba alaiyyahonki ki dan bashi minti biyu sai ki sauke.

  5. Ana iya ci da tuwon shinkafa,semo,masa,sinasir da sauransu.

    Miyar gyada recipe step 5 photo

Ingredients

  1. Gyada cup 1
  2. Manja
  3. Daddawa
  4. Jajjagen kayan miya
  5. Garlic da ginger paste
  6. Albasa
  7. Tafashen nama da kashi
  8. Ganda
  9. Cray fish
  10. Seasoning
  11. Maggi
  12. Alaiyyaho
  13. Gishiri

Related Recipes

Kalallaba

Kalallaba

Alawar madara ta condensed milk

Alawar madara ta condensed milk

Spicy sausage samosa rolls

Spicy sausage samosa rolls

Yoghurt

Yoghurt

Left over stir fried rice

Left over stir fried rice

Focaccia bread

Focaccia bread

KFC Chicken

KFC Chicken

Homemade buttermilk

Homemade buttermilk