Sai ki dora ruwan gyadarki a wuta ya tafaso.ki barshi ya dan tafasa saboda gafin gyadar ya wuce, amma asa ido kar ya tafaso ya zube.sai ki samu roba da zaki dama kunun ciki sai ki dibi kullunki dai dai yadda kikeso sai ki dama shi da wannan ruwan cucumber da kika tace.idan ruwan gyadar ya tafasa gafin ya fita sai ki sheka kan kullun ki juya.