Tuwon alkama da semo da miyar kubewa

Source : Zaki Tafasa Ruwa Ki Rage Kadan Saiki Dama Garin Alkama Ya Kasance Dashi Zakiyi Talgi Saiki Zuba Cikin Tukunyar Kina Juyawa Saiki Rufe Amma Ba Dukabas...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : March 22, 2026

Step:

  1. Zaki tafasa ruwa ki rage kadan, saiki dama garin alkama ya kasance dashi Zakiyi talgi, saiki zuba cikin tukunyar kina juyawa, saiki rufe Amma ba dukaba

  2. Saiki barshi ya dahu, inya dahu zakiga yana kumfa shine alamar dahuwanshi, saiki rika sa semo kina juyawa haryayi taurin da kikeso saiki yayyafa ruwan zafi kadan ki rufe ki barshi ya turara kamar na minti 5 saiki kwashe.

  3. Kisa ruwa daidai a pot din Miya, kisa daddawa ki barshi ya tafasa saikisa maggi 1, ki bashi kamar 2 minutes saiki zuba kubewarki da kika yayyanka kanana

  4. Saiki sa whisker ki juya sosai, saiki barshi ta dahu kamar minti 3 xuwa 5 saiki sauke

  5. In zakici saiki hada da hadaddiyar stew dinki Wanda yaji kifi da kassa shikenan aci tuwo lafiya


Ingredients

  1. 1 cup Alkama
  2. 2 cups Semo
  3. Kubewa
  4. Stew
  5. Daddawa
  6. 1 Maggi

Related Recipes

Indomie

Indomie

Indomie mai tattasai da albasa

Indomie mai tattasai da albasa

Taliya da wake

Taliya da wake

Spinach pudding

Spinach pudding

Dan sulub

Dan sulub

Faten doya da alanyahu

Faten doya da alanyahu

Semo and fresh okro

Semo and fresh okro

Farfesun kifi

Farfesun kifi