Source : A Sami Gero A Surfa Shi A Cire Dusar Sai A Wanke Shi Tass A Rege A Cire Tsakuwar Sannan A Dora Tukunya Akan Wuta Sai A Zuba Geron A Saka Dakakkiyar Ci...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : July 10, 2026
Step:
A sami gero a surfa shi a cire dusar. Sai a wanke shi tass. A rege a cire tsakuwar.
Sannan a dora tukunya akan wuta sai a zuba geron a saka dakakkiyar citta Rabin karamin cokali a zuba wadataccen ruwa Wanda zai dafashi ya yi laushi, Idan ya dahuwa sai a sauke.
Idan ya dahu za aga yayi kauri ruwan cikin, sai A juye shi a Kofi ko bowl guda 2, sannan a kawo madarar gari kowanne a zuba masa cokali 2, a zuba Zuma da flavour. Sai a kawo kwakwa a watsa akai a juya.
A sha da duminsa, yanada dadi sosai ga kara lafiya. Kasancewar ya kunshi sinadarai masu Gina jiki. Gero, kwakwa da zuma.