Source : A Sami Gero A Surface A Cire Dusar Sannan A Wanke Shi A Rege A Fitar Da Tsakuwar Sai A Jika Shi Na Mintuna 30 Sannan A Yi Amfani Da Blender Me Karfin Ma...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : May 23, 2026
Step:
A sami gero a surface a cire dusar sannan a wanke shi a rege a fitar da tsakuwar sai a jika shi na mintuna 30.
Sannan a yi amfani da blender me karfin markade a markada yayi laushi sosai, ko a kai inji a markado.
Idan an markado sai a zuba yist a juya sosai a tabbatar ya samu. Sannan a rufe a dakashi a rana ko GU me dumi ya tashi na tsawon awa 2 ko fi.
Bayan ya tashi sai a dauko za a ga yayi kwai a ciki alamar ya tashi kenan. Sai a kawo karkashi da kubewa a zuba a ciki
Sannan a zuba dafaffen gero a ciki a juya sosai, sai a zuba albasa da magi da gishiri a juya Idan ya juyi sai a dandano naji Idan akwai tsami sai a saka bakar hoda karamin cokali 1 a juya.
A Dora tanda (kaskon yin waina) a zuba mai Idan yayi zafi sai a dunga zuba kullin a ci. Idan ya soyu sai a juya gefe. A dunga kwashewa a kwano ko roba ta sha iska har a gama.
A wanke kabeji, Korean tattasai, tumatir, guriji da albasa a yayyankasu yanda ake so a tsane a kwalanda. Sai a sami kwano a zuba wainar, sannan a barbada mata kuli kuli sannan a yaryada mai.
Sannan a zuba kabeji, tumatir, Korean tattasai, albasa da guriji. Sannan a sake saka wainar, a barbada kuli a zuba mai sannan kayan kabejin haka za ayi har a zuba yawan da ake so.
Shikenan sai a rufe. a ci ta da kunu ko da lemo tanada dadi sosai.