Source : Ga Kayayyakin Hadin Nan A Wanke Salak Da Gishiri D Ruwa A Rabashi Gida 2 A Tsane A Kwalanda Idan Ya Tsane Sai A Juye A Abu A Dora Kaskon Suya A Zuba Ma...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : April 6, 2026
Step:
Ga kayayyakin hadin nan.
A wanke salak da gishiri d ruwa a rabashi gida 2 a tsane a kwalanda, Idan ya tsane sai a juye a Abu.
A Dora kaskon suya a zuba mai kadan sannan a kawo yankakkiyar albasa a zuba a saka magi da Dan ruwa Idan ta dahuwa ruwa ya hade da albasa sai a sauke a juya a kwano Idan ya sha iska sai a zuba cream salad da ketchup a juya.
A Dora abin suya a kan wuta a saka mai Idan yayi zafi a FASA kwai a kada a sa magi a soya, Idan ya fara soyuwa sai a zuba dambun nama ko na kaza a juya su hade sai a kwashe.
A yayyanka burodi sai a dauko hadin albasannan a shafa akai, a jera tumatir da gurijin bature, sannan a jera ganyen salak, sannan a zuba hadin kwai da dambu. Sai a kawo yankakken burodi a rufa akai. Haka za ayi Tayi har a gama.
Sannan a saka a cikin faranta. Za a iya cinsa da lemo ko a sha da shayi musamman bunu...!!!