Bayan an barzo mini shinkafa sai na diba daidai yanda zaici steamer din, na wanke da ruwa na tsane ruwan. Sannan na zuba soyayyen mai kamar cokali 3 na sa Maggie shima ba da yawa ba da Dan gishiri kadan na jujjuya na jefa icen kirfa sannan na juye a cikin steamer din dama na Dora akan wuta ruwan ya yi zafi sai na sa buhu a saman na rufe da murfin sannan na Dora Abu me nauyu.