Source : Da Farko Zaki Fara Da Feraye Dankali Kiyi Masa Yankan Gida Gida Sai Ki Dora Ruwa Idan Ya Tafasa Ki Zuba Macaroni A Ciki Ki Diga Mai Kadan Sai Ki Rufei...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : February 19, 2026
Step:
Da farko zaki fara da feraye dankali kiyi Masa yankan gida gida. Sai ki Dora ruwa idan ya tafasa ki zuba macaroni a ciki, ki diga Mai kadan sai ki rufe
Idna ya fara tafasa sai ki zuba danklain su tafaso tare. Kiyi musu Rabin dahuwa ki wanke ki tsane sai ki ajiye a gefe
Sai a yayyanka Kara's a wanke da koren wake Suma a tafasa da Dan gishiri a ajiye
Sai a Dora tukunya a zuba mai sannan a yyayanka albasa kadan akai idan ta Dan kwanta sai a zuba jajjagen tarugu da albasa akai a soya a kawo markaden kayan Miya cokali 2 a zuba akai
Sai a kawo Naman kazar a yayyanka a watsa akai sai a tsiada ruwa kadan wanda dai Zai karasa dafa taliyar. A saka kayan dandano da kayan kamshi. Idan Ana son tafarnuwa ma a saka
Sannan a yanka albaasa slice a watsa kan macaroni sai a kawo a zuba akan harin a rage wuta sosai sai a jujjuya sama sama a rufe a barshi ya turara sai a kashe.
A smai biredin shawarma a zuba hadin sai a nannade a soke da toothpick. Sai a soka almond dan ya bada shaawa