Hadin dafaffen gero na musamman

Source : A Sami Gero A Surfa Shi A Cire Dusar Sai A Wanke Shi Tass A Rege A Cire Tsakuwar Sannan A Dora Tukunya Akan Wuta Sai A Zuba Geron A Saka Dakakkiyar Ci...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : July 10, 2026

Step:

  1. A sami gero a surfa shi a cire dusar. Sai a wanke shi tass. A rege a cire tsakuwar.

  2. Sannan a dora tukunya akan wuta sai a zuba geron a saka dakakkiyar citta Rabin karamin cokali a zuba wadataccen ruwa Wanda zai dafashi ya yi laushi, Idan ya dahuwa sai a sauke.

  3. Idan ya dahu za aga yayi kauri ruwan cikin, sai A juye shi a Kofi ko bowl guda 2, sannan a kawo madarar gari kowanne a zuba masa cokali 2, a zuba Zuma da flavour. Sai a kawo kwakwa a watsa akai a juya.

  4. A sha da duminsa, yanada dadi sosai ga kara lafiya. Kasancewar ya kunshi sinadarai masu Gina jiki. Gero, kwakwa da zuma.

    Hadin dafaffen gero na musammanmatakin girki4 hoto

Ingredients

  1. Surfaffen gero Rabin kofi
  2. Madara cokali 4
  3. Zuma cokali 4
  4. Kwakwa cokali 6
  5. Vanilla flavor karamin cokali 1
  6. cokali Dakakkiyar citta Rabin karamin

Related Recipes

Mummuki bread

Mummuki bread

Coconut noodles

Coconut noodles

No oven cake

No oven cake

Taliya da macaroni me alayyahu da dambun nama

Taliya da macaroni me alayyahu da dambun nama

Sandwich a saukake

Sandwich a saukake

Hadin dafaffen gero na musamman

Hadin dafaffen gero na musamman

Juice din lemon Zaki da karas

Juice din lemon Zaki da karas

Potatoes patties

Potatoes patties