Kunun madara

Source : Ga Kayayyakin Da Ake Bukataa Sami Tukunya Me Tsafta Sannan A Zuba Madarar A Ciki Sai A Zuba Ruwa A Damata Har Sai Ta Damu Ta Zama Babu Gudaji A Dora T...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : April 26, 2026

Step:

  1. Ga kayayyakin da ake bukata

    Kunun madaramatakin girki1 hoto
  2. A sami tukunya me tsafta, sannan a zuba madarar a ciki, sai a zuba ruwa a damata har sai ta damu ta zama babu gudaji.

    Kunun madaramatakin girki2 hoto
  3. A Dora tukunyar madarar akan wuta a zuba kus-kus din akai a kawo sukari shima a zuba akai sai a fara juyawa sannan a barshi yayi ta dahuwa. A kula a zuba a tukunya me Dan girma sbd Idan ya tafaso zai zube.

    Kunun madaramatakin girki3 hoto Kunun madaramatakin girki3 hoto
  4. Idan aka taba kus kus din akaji ya dahu za aga madarar ta danyi kauri.

    Kunun madaramatakin girki4 hoto
  5. A zuba fulawa a kwano a zuba ruwa a dama ta Kar tayi ruwa ruwa sannan Kar tayi kauri, sannan a zuba filebo a ciki a juya.

    Kunun madaramatakin girki5 hoto Kunun madaramatakin girki5 hoto
  6. Idan ya damu babu gudaje sai a rage wutar a kawo damammiyar fulawar a zuba akan madarar a juya za a ga yayi kauri sai a kashe wutar ayi ta juyawa har sai ya hade ya zama Abu daya, za aji kamshi yanata tashi sai a sauke.

  7. A wanke dabino a cire kwallayen sai a rarrabashi kanana. Sannan a zuba kunun a mazubi sai a kawo dabinon a watsa akai. A sha da zafinsa Idan ya sha iska bazai yi dadi sosai ba.

    Kunun madaramatakin girki7 hoto Kunun madaramatakin girki7 hoto

Ingredients

  1. 1 Madara Kofi
  2. Fulawa 1/2 kofi
  3. Sukari 1/3 kofi
  4. Kus-kus manya 1/4 kofi
  5. 1/3 cokali Filebo na kwakwa
  6. 1/3 cokali Filebo na vanilla
  7. Ruwa Kofi 4 (measuring cup)
  8. Dabino guda 5 manya

Related Recipes

Faten dankalin turawa me alayyahu

Faten dankalin turawa me alayyahu

Kwadon yakuwa

Kwadon yakuwa

Lemon goba na musamman me whipping cream

Lemon goba na musamman me whipping cream

Fried meat pie

Fried meat pie

Roasted tomato garlic sauce

Roasted tomato garlic sauce

Taliya da macaroni me alayyahu da dambun nama

Taliya da macaroni me alayyahu da dambun nama

Dan-tamatsitsi

Dan-tamatsitsi

Yadda ake hada awaraTofu

Yadda ake hada awaraTofu