Alale mai hadin kwai

Source : Ki Surfa Wake Ki Wanke Ya Fita Sosai Saiki Wanke Tarugu Da Tattasai Da Albasa Kisa A Cikin Waken Saiki Kai Markade Bayan An Markada Saiki Sa Mai Ma...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : April 24, 2026

Step:

  1. Ki surfa wake, ki wanke ya fita sosai, saiki wanke tarugu da tattasai da albasa kisa a cikin waken, saiki kai markade.

    Alale mai hadin kwaimatakin girki1 hoto
  2. Bayan an markada, saiki sa mai, maggi, gishiri kadan, curry da kayan kamshi, saiki jiya sosai, kayan ya hade

    Alale mai hadin kwaimatakin girki2 hoto Alale mai hadin kwaimatakin girki2 hoto
  3. Saiki samu gwangwanaye masu kyau da tsafta, saiki shafa mai a cikin gwangwanin, saiki zuba hadin alalenki a ciki, amma bada yawa zaki sa ba, rabin gwangwanin zakisa

    Alale mai hadin kwaimatakin girki3 hoto Alale mai hadin kwaimatakin girki3 hoto
  4. Saiki dora ruwa a tukunya, amma ruwan kadan, saiki barsu su tafasa, saiki kawo gwangwanin da kk sa alalenki saiki sa a cikin tukunyar, ki kula karkisa ruwa da yawa, saiki barshi ya dahu na tsawon minti ashirin

  5. Saiki kada kwai kisa kayan kamshi da maggi da curry, kisa jajjagaggen tarugu da albasa, kisa alanyahu kadan saiki kada

    Alale mai hadin kwaimatakin girki5 hoto
  6. Idan alalanki yayi minti ashirin saiki fitar, kisa hadin kwanki, a cikin ko wanne gwangwani, saiki koma mayarwa a wuta yayi minti 10 saiki sauke ki cire shikenan

    Alale mai hadin kwaimatakin girki6 hoto Alale mai hadin kwaimatakin girki6 hoto Alale mai hadin kwaimatakin girki6 hoto
  7. Zaki iya ci haka kuma zaki iya ci da miya, yadda nayi miyar, na soya mai nasa yankakken tumatir, nasa jajjagaggen tarugu da albasa da maggi da kori da kayan kamshi saina juya na rufe, minti 5 saina sauke, aci dadi lafiya

    Alale mai hadin kwaimatakin girki7 hoto Alale mai hadin kwaimatakin girki7 hoto Alale mai hadin kwaimatakin girki7 hoto
  8. Ga irin gwangwanin da nayi alalen dashi, amma ba dole sai irinshi ba, zaki iya yi da wanda kike da

    Alale mai hadin kwaimatakin girki8 hoto Alale mai hadin kwaimatakin girki8 hoto

Ingredients

  1. 2 Wake kofi
  2. 1 Tattasai
  3. 1 Albasa
  4. 3 Tarugu
  5. 3 Maggi
  6. Korri rabin leda
  7. Manja da man gyada
  8. 3 Kwai
  9. Tarugu da albasa cokali 1
  10. Alanyahu kadan
  11. Kayan kamshi

Related Recipes

Miyar taushe

Miyar taushe

Kwadon shinkafa da latas

Kwadon shinkafa da latas

Hadin kayan marmari

Hadin kayan marmari

Jollop rice and salad with eggs

Jollop rice and salad with eggs

Dan wake

Dan wake

Yam balls step by step on how to make it

Yam balls step by step on how to make it

Tuwon shinkafa miyar kubewa

Tuwon shinkafa miyar kubewa

Kwadon salad

Kwadon salad