Zaa dora tukunya a wuta a zuba manja idan yayi zafi sai a zuba jajjagen a soyasu a zuba maggi salt garin tafarnuwa a gauraya sannan a kara ruwa a rufe tukunyar a barshi ya ya tafasa sai a dauko shinkafar da aka barza a wanke ta sai a zuba cikin tukunyar a juya sannan a rage wuta dan ya dahu yadda ake so.