Source : A Wanke Nama Ya Fita Sosai Sannan A Zuba A Tukunya A Zuba Ruwa A Dora Akan Wuta A Saka Kayan Kamshi Gishiri Kadan Albasa Magi Hade Da Kori Idan Ya...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : April 3, 2026
Step:
A wanke nama ya fita sosai, sannan a zuba a tukunya a zuba ruwa a Dora akan wuta, a saka kayan kamshi, gishiri kadan, albasa, magi, hade da kori Idan ya dahuwa sai a ajiye a gefe.
Dora tukunya akan wuta, zuba mai Dan daidai, yayyanka albasa a ciki Idan yayi zafi soya naman sama sama, Zuba jajjajgaggen attaruhu da albasa a soya na Tsohon minti 5, sannan a zuba ruwan dahuwar naman Idan baida yawa sai a kara da ruwan dumi a rufe.
Idan ya tafasa sai a zuba kayan dandano, curry, kayan kamshi sannan a kawo tsaki a wanke shi tas a zuba akai a rage wuta, Idan ya rage mintuna kamar 10 zuwa 15 a sauke sai a zuba yayyankakken dankalin Hausa a ciki su karasa dahuwa tare.
A zuba a faranti sai a tsinki ganyen na'a na'a a sa akai sabida ya bawa girkin abin shaawa.