Homemade Pasta

Source : Ki Samu Roba Madaidaiciya Seh Ki Zuba Flawa Da Gishiri Ki Juya Da Chokali Meh Yatsu Sannan Kiyi Rami A Tsakiyar Flawar Seh Ki Fasa Kwanki Ki Zuba A Tsak...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : April 21, 2026

Step:

  1. Ki samu roba madaidaiciya seh ki zuba flawa da gishiri ki juya da chokali meh yatsu.sannan kiyi rami a tsakiyar flawar seh ki fasa kwanki ki zuba a tsakiyar flawar cikin ramin da kikayi.seh ki sa chokali meh yatsu ki rika kwabawa da shi har ruwan kwan ya hade da flawar.

    Homemade Pastamatakin girki1 hoto Homemade Pastamatakin girki1 hoto Homemade Pastamatakin girki1 hoto
  2. Idan ya hade amma da sauran flawa kadan seh ki juye hadin a kan work surface dinki da sauran flawar seh ki cigaba da murzawa da hannun ki har seh ya hade.idan ya hade seh ki cigaba da murzawa kina kneading har seh ta murzu ta hada jikinta,seh ki sa wuka ki tsaga tsakiyar flawar idan kinga cikin ta yayi sumul ba ramuka toh tayi amma idan da ramuka ki cigaba da murzawa har seh tayi sumul.

    Homemade Pastamatakin girki2 hoto Homemade Pastamatakin girki2 hoto Homemade Pastamatakin girki2 hoto
  3. Seh ki sa kwabin a roba ki rufe ki bashi kamar minti 30 sannan ki dakko ki raba gida 4 seh ki dauki guda daya ki fadada shi da hannunki seh ki barbada flawa ki saka shi a cikin injin a lamba daya wurin fadi ki fadada shi,zakiyi haka kamar sau uku sannan ki ninka shi sau uku kamar ninkin wasika seh ki kara saka shi ki fadada sannan ki fara kara lamba kina fadadawa zaki ga tayi falan falan tayi tsawo idan kaurinshi yayi miki seh ki barshi haka.

    Homemade Pastamatakin girki3 hoto Homemade Pastamatakin girki3 hoto
  4. Sannan ki raba shi yadda kike son tsawon taliyar ta kasance (kamar inci 12)seh ki saka a wurin da zeh yanka miki a jikin injin din ki yanka.Haka zakiyi da sauran har ki gama.

    Homemade Pastamatakin girki4 hoto Homemade Pastamatakin girki4 hoto Homemade Pastamatakin girki4 hoto
  5. Kina iya shanyata a jikin igiyar shanya,ko a buhu ko tabarma meh tsafta ko bayan kujera ya bushe.Idan baki da injin taliya kina iya amfani da wuka meh kaifi ki yayyanka bayan kin murzata kin fadada da rolling pin.

    Homemade Pastamatakin girki5 hoto Homemade Pastamatakin girki5 hoto

Ingredients

  1. Kofi 2 na flawa(da karin kadan na murji)
  2. Kwai guda 3(manya)
  3. chokali Gishiri rabin karamin
  4. Injin taliya(ko wuka idan baki da shi)

Related Recipes

Chocolate Cupcakes

Chocolate Cupcakes

Bredin kabewa meh rose

Bredin kabewa meh rose

Dan wake

Dan wake

Home made icing sugar

Home made icing sugar

Potato Fritata

Potato Fritata

Left over stir fried rice

Left over stir fried rice

Mango juice with tamarind

Mango juice with tamarind

Parpesun kaza meh dankali

Parpesun kaza meh dankali