Source : Da Farko Ki Samu Kofi Ki Zuba Ruwan Dumi Sugar Da Yeast Ki Barshi Yayi Kaman Minti 5 Ya Kumburo Seh Ki Samu Roba Ki Zuba Flour Da Gishiri Ki Danyi Rami ...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by mhhadejia
at : August 6, 2026
Step:
Da farko ki samu kofi ki zuba ruwan dumi,sugar da yeast ki barshi yayi kaman minti 5 ya kumburo.seh ki samu roba ki zuba flour da gishiri ki danyi rami a tsakiya seh ki zuba hadin yeast da yogurt da mai,ki kwaba shi har seh ya hade jikinsa.
Seh ki samu kitchen towel ki dan jika shi ki matse seh ki rufe kwabin ki sa a waje meh dumi ki barshi ya tashi kamar tsawon hour 1.Bayan kwabinki ya tashi seh ki rabashi gida 8.
Seh ki mulmula kowanne da hannunki akan work surface kamar kwallo seh ki dauki daya ki rufe sauran da kitchen towel saboda kar su bushe.ki barbada flour kadan kan surface din seh ki fadada kwabin yayi fadi.seh ki dauko narkakken botan ki ki yi grating tafarnuwan a ciki ki shafa saman naan din.
Ki daura frying pan a wuta idan yayi zafi seh ki dauko kwabin nan dakika fadada kika shafawa bota ki dora akan frying ban din wajen botan ya kasance a kasa seh kiyi sauri ki dauki kwanon silver meh fadi ko tukunya ki rufe shi,hakan zeh sa tururi ya gasa miki naan din kuma yayi laushi.
Idan yayi kamar minti 3ko4 seh ki samu kitchen cloth ki daga kwanon silver din seh ki juya daya gefen ya gasu(amma baza ki maida kwanon ba yanzu).idan ya gasu seh ki samu abu kisaka shi ki rufe da kitchen towel kar ya huce.Haka za kiyi da sauran har ki gama.Idan kin gama seh ki barbada ganyen cilantro a kai.Achi lfy.kina iya chi da curry sauce ko parpesu.