Source : Ki Samu Roba Ki Zuba Cocoa Sugar Flour Da Gishiri Ki Juya Sosai Ya Hade Seh Ki Samu Tukunya Karama Ki Dora Kan Wuta Ki Zuba Madara Seh Ki Saka Bota Ki...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by mhhadejia
at : July 29, 2026
Step:
Ki samu roba ki zuba cocoa,sugar,flour da gishiri ki juya sosai ya hade.
Seh ki samu tukunya karama ki dora kan wuta ki zuba madara,seh ki saka bota ki juya ya narke a kan wuta med flame.seh ki zuba vanilla.
Ki barshi ya tafaso seh ki zuba hadin cocoa kadan kadan kina juyawa. Seh ki barshi ya dahu minti biyar a wuta kadan kina meh juyashi koda yaushe kar ya kama.
Bayan minti biyar seh ki rage wuta sosai ki kara barinshi ya dahu na tsawon minti biyar kina juyawa akai akai.
Shikenan seh ki sauke ki barshi ya huce seh ki juye a roba meh murfi ki adana a fridge.kina iya amfani da shi wajen frosting cake ko donut ko ki zuba a kan ice cream.