Peanut burger

Source : Da Farko Ki Gyara Gyadarki Ki Tsince Dattin Da Marar Kyau Sai Ki Samu Roba Mai Girma Ki Juye Ciki Sai Ki Samu Wata Robar Ki Fasa Kwan Ki Zuba Sikari Mad...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : September 29, 2025

Step:

  1. Da farko ki gyara gyadarki ki tsince dattin da marar kyau sai ki samu roba mai girma ki juye ciki.sai ki samu wata robar ki fasa kwan ki zuba sikari,madara,gishiri,mai karamin chokali da flavour ki juya sosai har sikarin ya narke.

    Peanut burgermatakin girki1 hoto Peanut burgermatakin girki1 hoto Peanut burgermatakin girki1 hoto
  2. Sai ki samu wata robar ki zuba flour ki sa baking powder ki juya sosai.sai ki samu chokali ki rika diban ruwan kwan kina yaryadawa akan gyadar kamar chokali biyu sai ki dauki robar kina juya gyadar kina hausuno na kasan kamar dai kina bakace har ko ina ya hade.Daman ki samu tray ko newspaper kin shimfida a gabanki ta yadda idan kina juyawa kamar kina bakace flour da take fita zata zuba a kai.

    Peanut burgermatakin girki2 hoto Peanut burgermatakin girki2 hoto
  3. Bayan kin juya ko ina ya hade sai ki dibo flour shima da wani chokali daban ki barbada a kai shi ma ki juya ko ina ya hade.Haka za kiyi tayi har hadin kwan da flour ya kare.idan kin gama sai ki sa hannu ki rarraba wanda suka hade idan da bukatar kara flour idan da sauran danshin ruwan kwan sai ki kara barbadawa ki juya har sai ya kame jikin shi (kina iya amfani da flour da ta taru a tray din).

    Peanut burgermatakin girki3 hoto
  4. Bayan kin gama sai ki samu rariya ki na zuba gyadar kina tankadewa saboda sauran flour ta fita.Bayan kin gama sai ki daura man ki a wuta idan yayi zafi sai ki fara soya gyadar amma ba a cika ta a kaskon kuma ba a cika mata wuta kina juyawa akai akai har ta soyu.

    Peanut burgermatakin girki4 hoto Peanut burgermatakin girki4 hoto
  5. Gashi a nan tafara kama jikin ta.Idan ta soyu tayi golden sai ki kwashe a colander ta tsane haka zakiyi har ki gama.

    Peanut burgermatakin girki5 hoto Peanut burgermatakin girki5 hoto Peanut burgermatakin girki5 hoto

Ingredients

  1. Gyada kofi4
  2. rabin karamin chokali na gishiri
  3. Flour kofi 4 (da kari idan da bukata)
  4. 2 Kwai
  5. Peak milk ta ruwa 1/4 kofi
  6. Vanilla flavour karamin chokali 1
  7. Sikari kofi 1(ko yadda akeson zakin)
  8. Mai karamin chokali 1
  9. Mai na suya
  10. Rabin karamin chokali na baking powder

Related Recipes

Pizza sauce

Pizza sauce

Soft and fluffy puff puff

Soft and fluffy puff puff

Parpesun naman akwiya

Parpesun naman akwiya

Home made golden syrup

Home made golden syrup

Pasta rice jollof

Pasta rice jollof

Left over stir fried rice

Left over stir fried rice

Samosa pinweels/samosa bites

Samosa pinweels/samosa bites

Kalallaba

Kalallaba