Potato Fritata

Source : Da Farko Ki Fere Dankalin Ki Yanka Shi Kanana Seh Ki Wanke Ki Zuba A Tukunya Ki Zuba Ruwa Ya Sha Kanshi Ki Sa Gishiri Kadan Ki Tafasa Seh Ki Yanka Alba...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : January 27, 2026

Step:

  1. Da farko ki fere dankalin, ki yanka shi kanana seh ki wanke ki zuba a tukunya ki zuba ruwa ya sha kanshi ki sa gishiri kadan ki tafasa.seh ki yanka albasan da koran tattasan.shima tumatirin ki yanka shi yankan zagaye.

    Potato Fritatamatakin girki1 hoto
  2. Seh ki dora frying pan a wuta ki zuba mai kadan,seh ki zuba albasa ki soya sama sama sannan ki zuba tarugu.Idan ya dan soyu seh ki zuba sausage ki sa dandano da masoro ki dan soya kadan sannan ki zuba dankali.

    Potato Fritatamatakin girki2 hoto Potato Fritatamatakin girki2 hoto Potato Fritatamatakin girki2 hoto
  3. Ki juya sannan ki barshi ya dan soyu dankalin ya kama jikin shi.seh ki samu roba ki fasa kwan ki zuba garlic salt kadan ki kada.sannan ki zuba akan hadin dankalin,seh ki dan girgiza frying pan din kadan kwan ya samu koina.

    Potato Fritatamatakin girki3 hoto
  4. Seh ki samu murfi ki rufe ki rage wutan idan yayi kamar minti biyu ya dan kame seh ki jera tumatir din da koran tattasai ki rufe,sannan ki rage wutar kar ya kone.Idan ya kame seh ki samu faranti meh fadi ki kifa shi akan frying pan din seh ki juye a hankali,seh ki maida frying pan din wuta ki dakko farantin ki maida hadin a hankali daya gefen ma ya soyu.Idan yayi seh ki sake mai dashi kan farantin yadda kikayi dazu wurin hadin tumatirin ya dawo sama.shi kenan aci lafiya.

    Potato Fritatamatakin girki4 hoto Potato Fritatamatakin girki4 hoto

Ingredients

  1. 2 Dankali manya
  2. 3 Kwai
  3. 1 Koran tattasai
  4. Albasa 1(karama)
  5. 2 Sausage
  6. Tumatir 2(kanana)
  7. Tarugu
  8. Garlic salt
  9. Dandano
  10. Masoro

Related Recipes

Lemon Bundt cake

Lemon Bundt cake

Spicy crackers

Spicy crackers

Stuffed potato balls

Stuffed potato balls

Fluffy doughnuts

Fluffy doughnuts

Spicy sausage samosa rolls

Spicy sausage samosa rolls

Kunun tsamiya da kosai

Kunun tsamiya da kosai

Yoghurt na dafawa

Yoghurt na dafawa

Kunun gyada meh cucumber

Kunun gyada meh cucumber