Soyayyen kwai meh vegetables da bredi gashin frying pan

Source : Ki Hada Turmeric Chokali Daya Da Masoro Karamin Chokali Da Chitta 1/2 Karamin Chokali Ki Sa Maggi Daya Da Gishiri Kadan Ki Hadesu Waje Daya Ki Samu Roba...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : August 2, 2026

Step:

  1. Ki hada turmeric chokali daya da masoro karamin chokali da chitta 1/2 karamin chokali ki sa maggi daya da gishiri kadan ki hadesu waje daya ki samu roba ki juye duk sanda zaki soya kwai seh ki barbada a kai.

  2. Ki samu frying pan seh ki sa mai kadan ki fasa kwanki a ciki kar ki kada seh ki zuba tumatir,albasa koran tattasai(yankakke) a kai ki dan rage wutan kadan seh ki barbada hadin turmeric a kai.

  3. Idan ya soyu seh ki juya daya gefen a hankali ki kara barbada hadin turmeric a kai ki barshi ya soyu seh ki sa a plate.

  4. Seh ki dakko bredinki ki gasa a kan frying pan din duka gefe biyun.kina iya sha da tea ko ki ci haka.


Ingredients

  1. Kwai guda biyu
  2. Bredi yanka biyu
  3. Tumatir karami
  4. 1 Koran tattasai karami
  5. 1/2 Albasa karama
  6. Dandano
  7. Turmeric, masoro da chitta (gari)
  8. Gishiri

Related Recipes

Miyar gyada

Miyar gyada

Alkubus na alkama

Alkubus na alkama

Baguette bread

Baguette bread

Lemun cucumber da lemu

Lemun cucumber da lemu

Mango juice with tamarind

Mango juice with tamarind

Burabuskon alkama meh kayan lambu

Burabuskon alkama meh kayan lambu

Pasta rice jollof

Pasta rice jollof

Mandula

Mandula