Faten tsakin shinkafa

Source : Da Farko Ki Gyara Namanki Da Kashi Ki Wanke Ki Zuba A Tukunya Sai Ki Yanka Masa Albasa Ki Zuba Dan Citta Da Tafarnuwa Da Maggi Da Gishiri Ki Barshi Ya D...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : April 28, 2026

Step:

  1. Da farko ki gyara namanki da kashi ki wanke ki zuba a tukunya sai ki yanka masa albasa ki zuba dan citta da tafarnuwa da maggi da gishiri ki barshi ya dahu.

  2. Ki gyara ganyayyakin ki ki wanke tas ki tsane sai ki wanke tsakin ki shima ki tsane.

  3. Idan namanki ya dahu sai ki zuba manja akai da kayan miya ki tsaida ruwa daidai yadda kikeson fatenki sai ki zuba kayan kamshi da daddawa da dandano ki barshi ya tafaso.

  4. Idan ya tafaso ya dan dahu sai ki zuba tsakin ki ki juya ki rage wutan kina juyawa akai akai kar ya kama idan yafara kauri sai ki zuba yakuwa da lawashi ki juya ki barshi yadan sulala sai ki zuba alaiyahunki a karshe bayan yayi laushi sai ki bashi kamar minti biyar.sai ki sauke shikenan fate ya kamma.


Ingredients

  1. Tsakin shinkafa
  2. Jajjagen kayan miya
  3. Nama da kashi
  4. Alaiyaho
  5. Yakuwa
  6. Ganyen albasa
  7. Tafarnuwa da citta dakakke
  8. Daddawa
  9. Kayan dandano
  10. Kayan kamshi
  11. Albasa
  12. Manja

Related Recipes

Brownie pizza

Brownie pizza

Turtle cookies

Turtle cookies

Chocolate sauce/frosting

Chocolate sauce/frosting

Yoghurt na dafawa

Yoghurt na dafawa

Chicken pepper soup

Chicken pepper soup

Golden yam with fish sauce

Golden yam with fish sauce

Spicy sausage samosa rolls

Spicy sausage samosa rolls

Sauce din naman akwiya

Sauce din naman akwiya