Source : Da Farko Ki Daura Tukunya Kan Wuta Sai Ki Zuba Butter Idan Ya Narke Sai Ki Sa Albasa Da Garlic Ginger Paste Idan Albasar Ta Soyu Sai Ki Zuba Flour Ki Ju...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by mhhadejia
at : May 13, 2026
Step:
Da farko ki daura tukunya kan wuta sai ki zuba butter idan ya narke sai ki sa albasa da garlic ginger paste.
Idan albasar ta soyu sai ki zuba flour ki juya ya hade da albasar ki barshi ya dahu kamar minti 2ko3. Sai ki zuba ruwan namanki ki juya sosai saboda kar ya dunkule ki kawo nikakken namanki ki zuba kisa dandano da gishiri ki rage wutan.
Sai ki zuba madara ki juya sosai idan yayi kauri kina iya kara ruwa daidai kaurin da kikeso ki rage wutan sosai sai ki zuba alaiyahonki ki rufe ki bashi kamar minti uku sai ki sauke.Ana iya sha haka ko ki hada da kowane irin nauin bredi.
Ingredients
1/4 cup Flour
2 cup Madara
2 cup Alaiyaho yankakke
Butter cokali 4
4 Ruwan tafashen nama ko kaza kofi
Madara kofi 1da rabi (in ba fresh sai a hada na gari da ruwa)