Miyar egusi

Source : Dafarko Zaki Dora Mai A Wuta Kisa Albasa Ki Soya Saiki Sa Kayan Miya Ki Juya Saiki Bari Su Fara Soyuwaki Juye Egusi A Bowl Kisa Ruwa Ki Dama Saiki Ri...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : April 2, 2026

Step:

  1. Dafarko zaki dora mai a wuta kisa albasa ki soya, saiki sa kayan miya ki juya, saiki bari su fara soyuwa

  2. Ki juye egusi a bowl kisa ruwa ki dama, saiki Rika diba kina zubawa acikin kayan miyar da kike soyawa

  3. Saiki rage wuta, kibashi kamar minti 5 saiki juya, zakiga yayi kamar awara, saiki sa ruwa kamar 6 table spoon

  4. Saiki sa kayan kamshi da Maggi da curry, ki juya sosai, saiki sa alanyahu da albasa ki juya

  5. Saiki rufe ki bashi kamar minti 3 saiki sauke shikenan sai kici da tuwon da kikeso, ni naci nawa da tuwon alkama da semo

    Miyar egusimatakin girki5 hoto

Ingredients

  1. Kayan miya
  2. Manja
  3. Kayan kamshi
  4. Alanyahu
  5. Egusi
  6. Albasa
  7. Maggi da curry

Related Recipes

Meat balls

Meat balls

Hadadden zobo

Hadadden zobo

Gurasa bandashe

Gurasa bandashe

Beef and egg rolls

Beef and egg rolls

Fruit salad 2

Fruit salad 2

Macaroni and minced meat

Macaroni and minced meat

Garau garau

Garau garau

Farfesun kifi

Farfesun kifi