Faten acca

Source : Da Farko Ki Dora Tafashen Namanki Ki Yanka Masa Albasa Ki Sa Dandano Da Dan Gishiri Kadan Ki Sa Chitta Da Tafarnuwa Ki Zuba Ruwa Ya Tafasa Idan Namanki ...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : October 25, 2025

Step:

  1. Da farko ki dora tafashen namanki ki yanka masa albasa ki sa dandano da dan gishiri kadan ki sa chitta da tafarnuwa ki zuba ruwa ya tafasa.

  2. Idan namanki yayi sai ki zuba kayan miyanki a kai,ki zuba manja,daddawa,dandano,kayan kanshi sai ki zuba ruwa dai dai yadda kike son yawan fatenki.

  3. Ki gyara alaiyahonki ki wanke shi,yakuwa ma da ganyen albasa haka zaki musu kowanne daban sai ki aje gefe.

  4. Idan ruwan sanwarki ya dahu sai ki rege accar ki ki wanke tas,sai ki zuba ki juya ki dan rage wutar.idan ya fara kauri sai ki zuba yakuwa da ganyen albasa ki barsu su dahu.idan da bukatan karin dandano ko gishiri sai ki kara. Idan yakuwar da ganyen albasan sun dan dahu sai ki zuba alaiyahonki ki juya ki rufe ki barshi kamar minti biyar sai ki sauke.


Ingredients

  1. Acca
  2. Jajjagen kayan miya
  3. nama da kashi
  4. Daddawa
  5. Alaiyaho
  6. Yakuwa
  7. Ganyen albasa
  8. tafarnuwa Chitta da
  9. Dandano
  10. Kayan kanshi
  11. Gishiri
  12. Manja
  13. Ruwa

Related Recipes

Baguette bread

Baguette bread

Left over stir fried rice

Left over stir fried rice

Spicy crackers

Spicy crackers

Mandula

Mandula

Kalallaba

Kalallaba

Home made vanilla and chocolate icecream

Home made vanilla and chocolate icecream

Dublan

Dublan

Pizza

Pizza