Source : Da Farko Ki Samu Plantain Dinki Yadda Kike Bukata Seh Ki Yanka Shi Kanana Ki Zuba A Blender Ki Sa Ruwa Kadan Kiyi Blending Har Yayi Laushi Idan Da Bukat...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by mhhadejia
at : February 9, 2026
Step:
Da farko ki samu plantain dinki yadda kike bukata seh ki yanka shi kanana ki zuba a blender ki sa ruwa kadan kiyi blending har yayi laushi idan da bukatar ki kara ruwa seh ki kara kadan amma kar ki cika ruwa.
Seh ki juye shi a tukunya ki dora akan wuta medium seh kiyi ta juya shi da muciya har seh ya fara danko alamun ya fara dahuwa kenan.
Seh ki sa mara ki gyara bakin tukunyar ki yayyafa ruwa kadan akai seh ki rage wutan ki rufe da foil paper ki barshi ya turara kamar minti 15.
Idan yayi kamar minti 15 seh ki tuka ki kwashe.Ana iya ci da duk miyar da ake so kamar ayayyo,kubewa,vegetable ko agushi.