Dublan

Source : Da Farko Ki Samu Roba Ki Zuba Yeast Sugar Chokali 1 Ruwan Dumi Chokali 1 Bota Mai Chokali 1da Madara Sai Ki Juya Ya Hade Sosai Idan Ya Hade Sai Ki Zuba ...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : October 14, 2025

Step:

  1. Da farko ki samu roba ki zuba yeast,sugar chokali 1,ruwan dumi chokali 1,bota,mai chokali 1da madara sai ki juya ya hade sosai.Idan ya hade sai ki zuba flawa ki kwaba ya hade jikinshi idan da sauran flawa kina iya yayyafa ruwa kamar chokali 1 ko 2 ki murza ya hade sosai sai ki rufe ki aje shi yayi kamar minti 15.

    Dublanmatakin girki1 hoto Dublanmatakin girki1 hoto Dublanmatakin girki1 hoto
  2. Bayan minti 15 sai ki dakko kwabin flawar ki ki kara murzawa sai ki raba gida 3.sai ki dauki daya ki murza shi da fadi sosai kuma yayi falan falan.kafin ki murza ki dan barbada corn flour a kai saboda kar ya dinga mannewa.

    Dublanmatakin girki2 hoto Dublanmatakin girki2 hoto Dublanmatakin girki2 hoto
  3. Sai ki samu takardar cardboard ki yanka rectangle shape ki dora akan flawar da kika fadada(saboda dublan dinki suyi girma daya)ki yanka dai dai fadin takardar da wuka ko pizza cutter.sai ki sa pizza cutter dinki ki tsatsaga daga gefe zuwa gefe har sama amma za ki dan bar tazara daga gefe gegen.

    Dublanmatakin girki3 hoto Dublanmatakin girki3 hoto Dublanmatakin girki3 hoto
  4. Sai ki samu ruwa ki dangwala a dan yatsan ki ki shafa a duka kusurwa hudun,sai ki ninka shi daga kusurwar sama ki hada da na kasa sai ki manne bakin.sai ki sake shafa ruwa a kusurwa hudun ki sake nunko shi ki shafa ruwa ta cikin gefen ki like shi.sai ki tattare gefen ki manne shi ya dan yi tsawo daya gefen ma ki mishi haka.

    Dublanmatakin girki4 hoto Dublanmatakin girki4 hoto Dublanmatakin girki4 hoto
  5. Sai ki bude tsakiyan ta cikin inda kika tsaga ki dakko gefen da kika manne yayi tsawo ki sako shi ta ciki sai ki zazzago shi zai baki shape kamar ganye.Haka zakiyi da sauran kwabin har ki gama.

    Dublanmatakin girki5 hoto Dublanmatakin girki5 hoto Dublanmatakin girki5 hoto
  6. Sai ki dora mai a wuta amma kar ki cika wuta,sai ki soya dublan dinki yayi ja sai ki kwashe.yadda zaki hada ruwan sikarin da zaki tsoma dublan din shine,ki zuba sikari kofi daya da rabi cikin tukunya sai ki zuba ruwa kofi daya ki sa ganyen na'a na'a da yayan fennel da lemun tsami rabi ki dora a wuta har sai yayi kauri ya fara danko sai ki kashe ki barshi ya huce.

    Dublanmatakin girki6 hoto Dublanmatakin girki6 hoto Dublanmatakin girki6 hoto
  7. Idan ya huce sai ki dakko dublan din kina tsoma shi cikin sikarin ki juya ko ina ya samu sai ki cire ki sa a roba ki sa wasu,haka zakiyi har ki gama.sai ki barbada yayan ridi da habbatussaudah Amfanin na'a na'a da yayan fennel a cikin sikarin zai bashi kamshi mai dadi.kina iya sa habba han(cardamom) ko star annise a maimakon su.

    Dublanmatakin girki7 hoto Dublanmatakin girki7 hoto

Ingredients

  1. 1/2 tsp yeast
  2. 1 tbsp ruwan dumi
  3. 1 tbsp sikari
  4. 2 tbsp bota
  5. 1 tbsp mai
  6. 1/4 tsp gishiri
  7. 1/2 kofi madara
  8. Kofi 2 na flawa
  9. Mai na suya
  10. Kofi 11/2 na sikari
  11. Ruwa kofi1
  12. Ganyen na'a na'a
  13. Yayyan fennel 1/2 karamin chokali
  14. 1/2 Lemun tsami
  15. Yayan ridi da habbatussaudah

Related Recipes

Hikimatayota

Hikimatayota

Kunun gyada meh cucumber

Kunun gyada meh cucumber

Left over stir fried rice

Left over stir fried rice

Miyar gyada

Miyar gyada

Kunun zaki

Kunun zaki

Toasted sandwich

Toasted sandwich

Fankaso

Fankaso

Lemun cucumber da lemu

Lemun cucumber da lemu