Source : Da Farko Ki Gyara Gyadarki Ki Tsince Dattin Da Marar Kyau Sai Ki Samu Roba Mai Girma Ki Juye Ciki Sai Ki Samu Wata Robar Ki Fasa Kwan Ki Zuba Sikari Mad...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by mhhadejia
at : September 29, 2025
Step:
Da farko ki gyara gyadarki ki tsince dattin da marar kyau sai ki samu roba mai girma ki juye ciki.sai ki samu wata robar ki fasa kwan ki zuba sikari,madara,gishiri,mai karamin chokali da flavour ki juya sosai har sikarin ya narke.
Sai ki samu wata robar ki zuba flour ki sa baking powder ki juya sosai.sai ki samu chokali ki rika diban ruwan kwan kina yaryadawa akan gyadar kamar chokali biyu sai ki dauki robar kina juya gyadar kina hausuno na kasan kamar dai kina bakace har ko ina ya hade.Daman ki samu tray ko newspaper kin shimfida a gabanki ta yadda idan kina juyawa kamar kina bakace flour da take fita zata zuba a kai.
Bayan kin juya ko ina ya hade sai ki dibo flour shima da wani chokali daban ki barbada a kai shi ma ki juya ko ina ya hade.Haka za kiyi tayi har hadin kwan da flour ya kare.idan kin gama sai ki sa hannu ki rarraba wanda suka hade idan da bukatar kara flour idan da sauran danshin ruwan kwan sai ki kara barbadawa ki juya har sai ya kame jikin shi (kina iya amfani da flour da ta taru a tray din).
Bayan kin gama sai ki samu rariya ki na zuba gyadar kina tankadewa saboda sauran flour ta fita.Bayan kin gama sai ki daura man ki a wuta idan yayi zafi sai ki fara soya gyadar amma ba a cika ta a kaskon kuma ba a cika mata wuta kina juyawa akai akai har ta soyu.
Gashi a nan tafara kama jikin ta.Idan ta soyu tayi golden sai ki kwashe a colander ta tsane haka zakiyi har ki gama.
Ingredients
Gyada kofi4
rabin karamin chokali na gishiri
Flour kofi 4 (da kari idan da bukata)
2 Kwai
Peak milk ta ruwa 1/4 kofi
Vanilla flavour karamin chokali 1
Sikari kofi 1(ko yadda akeson zakin)
Mai karamin chokali 1
Mai na suya
Rabin karamin chokali na baking powder
Related Recipes
Crunchy peanut cookies
Peanut burger
Boiled stir fried potatoes with chicken liver sauce