Seh ki zuba karas ki rufe ki bashi dan mintina karas din ya dahu.idan ya dahu seh ki zuba couscous dinki kina juyawa har ya shanye ruwan.seh ki sa foil paper ko buhu meh tsafta ki rufe ki kuma rufewa da murfin tukunyar seh ki kashe wutar ki barshi yayi kamar minti 15 tiririn ya karasa shi.seh ki sa chokali meh yatsu ki barbazashi cikin tukunyar kina dagowa a hankali zakiga yayi washar washar seh ki juye a cooler.kina iya chi da dage dage,parpesu ko duk miyar da kike so.