Lemon tsamiya, danyar citta da lemon zaki

Source : A Sami Roba Me Tsafta A Zuba Tsamiya Sannan A Zuba Ruwa A Wanketa Tass Sai A Dunka Tsamewa Ana Zubawa A Tukunya Me Tsafta Sai A Zuba Ruwa Ya Sha Kanta ...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : June 17, 2026

Step:

  1. A sami roba me tsafta a zuba tsamiya sannan a zuba ruwa a wanketa tass, sai a dunka tsamewa ana zubawa a tukunya me tsafta sai a zuba ruwa ya sha kanta a Dora akan wuta har sai ta dahu sai a sauke.

  2. A wanke danyar citta a tabbatar dattin da kasar ya fita, sai a yayyanka kanana a zuba ruwa a markada blender ko a goga da greeter, sannan a zuba ruwa a tace. Dusar zaki iya shanyawa kiyi amfani da ita as kayan kamshi.

  3. Sannan a wanke lemon zaki a bare sai a cire kwallayen da farin tsakiyar.(a kula da cire kwallayen, Idan ba a cire ba lemon zai baki wani dandano me daci Idan an markada). Sai a zuba a blender a markada a tace.

  4. A dauko roba me tsafta a tace tsamiya, sannan a zuba ruwan cittar, a kawo ruwan lemon a zuba, sai a saka kankara daga nan a kawo syrup sugar a zuba, Idan babu a zuba a normal sugar a juya. Za a ji yana kanshi Idan sukari yaji sai a zuzzuba a sha. Idan ba kankara za a iya sakawa a fridge yayi sanyi.

  5. Lemon yanada dadi ga kara lfy.

    Lemon tsamiya, danyar citta da lemon zakimatakin girki5 hoto

Ingredients

  1. 1 Tsamiya kofi
  2. 3 Danyar citta manya guda
  3. 5 Lemon bawo guda
  4. Sukari Dan dandano
  5. Kankara

Related Recipes

Paw-paw fruits salad bowl

Paw-paw fruits salad bowl

Tsiren zamani

Tsiren zamani

Rainbow fruit salad

Rainbow fruit salad

Almond fried Egg

Almond fried Egg

Dried carrot lavash heart shape

Dried carrot lavash heart shape

Potatoes ball me tsokar kaza

Potatoes ball me tsokar kaza

Wheat glazed doughnuts

Wheat glazed doughnuts

Peanut Burger

Peanut Burger