Source : A Gyara Gyada A Tsince Dattin A Tabbatar Ya Fita A Cire Wadanda Suka Bare Da Kuma Kananan Ya Zama Gyadar Guda Ce Me Kyau Kuma A Fasa Kwai A Roba A Saka...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : August 19, 2026
Step:
A gyara gyada a tsince dattin a tabbatar ya fita, a cire wadanda suka bare da kuma kananan ya zama gyadar guda ce me kyau kuma.
A FASA kwai a roba a saka sukari, madara, Baking powder da Dan gishiri a juya sosai har ya hade, a saka filebo ma a juya sai a ajiye a gefe
A sami babbar roba sosai ko Nace baho a juye gyadar a ciki, sai a Dan zuba hadin kwan a juya Idan koina yaji sai a barbada fulawa aita juyawa da robar ana yi ana rarraba wanda ya hade.
Haka za a maimaita har sai anga gyadar ta rufe babu alamar ana ganin gyadar.
Sannan a dora mai akan wuta Idan ya fara zafi sai a kwashe albasar a dunga zuba gyadar ana soyawa ana jujjuyawa don koina ya zama kala daya.
Idan ta soyu sai a kwashe a kwalanda a barta ta tsane. A barta ta sha iska tafi dadi.