Source : A Wanke Kazar Ayi Mata Yankan Gida 4 Sannan A Saka Lemon Tsami A Sake Wankewa A Tabbatar Ta Fita An Fitar Da Duk Dattin Da Yake Jikinta Sai A Tsane A K...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by Khady Dharuna
at : May 28, 2026
Step:
A wanke kazar ayi mata yankan gida 4 sannan a saka lemon tsami a sake wankewa a tabbatar ta fita an fitar da duk dattin da yake jikinta. Sai a tsane a kwalanda. Idan ya tsane sai a juye a tukunya. A zuba yankakkiyar albasa a raba lemon tsami 2 a zuba a ciki.
Sannan a wanke attaruhu shima a zuba akai
A goga danyar citta a zuba akai.
Sannan a saka curry, spices, seasoning, garin citta, hade da Maggie.
Sai a daka tafarnuwa Idan ana bukata a zuba akai, a watsa fennel seed sannan a Dan zuba ruwa kadan a rufe sai a Dora akan wuta.
A barta ta dahu sosai har ta fara farfashewa, sannan a bari ruwan ya kafe a jikin naman sai a sauke.
Sannan a sami karamar tabarya a dunga daddaka naman ya daku ba sosai ba dai. Sannan ba a cire kashin a haka zaki barta. Sai ki samu tray ki juye ki baza ya sha iska. A kula a wajen dahuwar zaki saka wadataccen magie yanda ba sai an kara daga baya ba.
Sai a Dora kaskon suya a wuta ayi amfani da me Dan girma, a zuba mai madaidaici a kawo albasa a zuba Idan yayi zafi sai a kwashe albasar a zuba naman a ciki a barbada kori sai a fara juyawa.
Ai ta juyawa amma sai anyi hakuri sbd Idan aka barshi suyar ba zatayi kyau ba. Idan ya fara kumfa to alama ya fara soyuwa ne, sai a cigaba da juyawa za abi kamshi yanata tashi.
Da zarar naman ya bar jikin kunfar man to shikenan dambun ya soyu sai a kashe.
Sannan a juye dambun a kwalandar karfe a dunga dannawa man ya ragu, sai A sami babban faranti me karfi Wanda bazai fashe ba, ko na silver ne sai a shimfida abin tata akai, sannan a juye dambun akai.
Daga nan sai a nannade shi kamar za a matse kulli sannan a Dora abu akai ni nayi amfani da murfin tukunya.... Sai a kuma Dora abu me nauyi kamar turmi a danne, za a ga man yanata fitowa.
Idan aka matse man sai a mayar da naman cikin turmi a Dan daddaka shi sama sama.
Sannan a juye a babbar roba, Idan ya sha iska zaki iya rage kashin ko kuma ki barshi Dan shima yanada dadin ci.