Dafadukar shinkafa da busashen kifi

Source : Da Farko Ki Gyara Kifinki Ki Cire Kayar Sai Ki Wanke Ki Aje Gefe Sai Ki Yanka Kayan Miyanki Daidai Misali Ki Yanka Albasa Ki Samu Tukunya Ki Dora A Wuta...

PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings

Sent by

at : May 28, 2026

Step:

  1. Da farko ki gyara kifinki ki cire kayar sai ki wanke ki aje gefe.sai ki yanka kayan miyanki daidai misali ki yanka albasa.

  2. Ki samu tukunya ki dora a wuta sai ki zuba mai ki sa albasa sai ki rage kadan.idan ya dan soyu sai kisa hadin citta da tafarnuwa nikakke.

  3. Idan ya dan soyu sai ki sa tumatir dinki na sachet ki barshi ya soyu tsamin ya fita sai ki zuba yankakken kayan miyanki kisa ganyen bay leaf ki soya.kisa dandano,gishiri da kayan kanshi idan ya soyu sai ki tsaida ruwa dai dai yadda zai dafa miki shinkafar.

  4. Idan ya tafaso sai ki wanke shinkafar ki zuba idan tafara laushi sai ki zuba kifinki da sauran albasa idan yana bukatar karin dandano ko ruwa sai ki kara ki barshi ya karasa dahuwa.


Ingredients

  1. 2 Shinkafa kofi
  2. 2 Busashen kifi madaidaita guda
  3. Tumatir,tattasai,tarugu,shambo
  4. Albasa
  5. 1 Tomato paste sachet
  6. Dandano
  7. Gishiri
  8. Kayan kanshi
  9. Mai
  10. Hadin citta da tafarnuwa dakakke
  11. Ganyen bay leaf

Related Recipes

Alkubus na alkama

Alkubus na alkama

KFC Chicken

KFC Chicken

Bredin kabewa meh rose

Bredin kabewa meh rose

Gizzard sauce

Gizzard sauce

Fura

Fura

Hanjin ligidi

Hanjin ligidi

Potato Fritata

Potato Fritata

Shelpek flat bread

Shelpek flat bread