Source : Da Farko Ki Wanke Tsamiyar Ki Sai Ki Jikata Da Ruwa Kadan Kafin Lokacin Da Zaki Dama Kunun Ki Idan Ta Jiku Sai Ki Tace Da Rariya Ki Kara Ruwa Kadan Kan ...
PreTime
more Minutes
CookTime
a few Minutes
Yield
Some Servings
Sent by mhhadejia
at : May 20, 2026
Step:
Da farko ki wanke tsamiyar ki sai ki jikata da ruwa kadan kafin lokacin da zaki dama kunun ki.Idan ta jiku sai ki tace da rariya ki kara ruwa kadan kan tsamiyar sai ki wanke hannun ki ki murtsiketa sai ki sake tacewa ki aje a gefe.
Ki dora ruwa ya tafasa sai ki samu garin kunun ki da yaji kayan kanshi sai ki dama da ruwan tsamiyar sai ki dibi gasarar kadan ki aje.Idan ruwanki ya tafasa sai ki zuba kan kullun ki juya ki rufe.ki barshi zuwa yan mintuna kadan sai ki dakko gasarar da kika rage ki zuba akai ki juya idan ya miki kauri dayawa kina iya kara ruwa kadan sai ki sa sugar ki juya.
Kosanki kuma ki surfa wakenki ki wanke dusar sai ki wanke shi tas ki rege sai ki jika.Idan ya jiku sai ki zuba tarugu,tattasai,shambo da albasa a kai sai ki sa citta da tafarnuwa a niko miki.
Idan an niko sai ki buga kullun sosai ki zuba gishiri, ajino kadan da baking powder kadan sai ki fasa kwai daya ko biyu ya danganta da yawan kullunki sai ki dan kara ruwa ki buga shi sosai.
Ki dora mai a wuta idan yayi zafi sai ki soya kosanki.